Isa ga babban shafi
Venezuela

Maduro ya nemi kariyar OPEC daga takunkuman Amurka

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya bukaci kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, ta bashi kariya daga takunkuman Amurka na haramtawa kasar saida danyen manta ga kasashe.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro.
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro. Reuters
Talla

Maduro ya yi gargadin cewa bayaga Venezuela, takunkuman za su iya shafar tattalin arzikin sauran kasashe masu arzikin na Man Fetur.

Bukatar ta shugaba Maduro na kunshe ne cikin wasikar da ya aikewa kungiyar OPEC a ranar 29 ga Janairun da ya gabata, kwana guda, bayan da Amurka ta kakabawa Venezuelan takunkumin haramta saida danyen manta zuwa kasashen waje, wanda sai a yanzu ta bayyana.

Takunkuman da aka sawa Venezuelan dai sun sanya dagawar farashin gangar danyen mai zuwa dala 62 daga 60.

Sai dai kawo yanzu kungiyar ta OPEC ba ta ce komai dangane da lamarin ba, la’akari da cewa, ta sha kaucewa shiga al’amuran siyasar kasa da kasa ko da kuwa ya shafi daya daga cikin manbobinta, kamar yadda taki amsa bukatar Iran a shekarar da ta gabata, lokacin da ta nemi agajinta kan takunkuman da Amurka ta kakabawa sashin hada-hadar danyen manta.

Sama da kasashen 40 da suka hada da Amurka, da wasu manyan kasashen yammacin Turai da na yankin Latin, sun amince da shugabancin jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, wanda ya nada kansa a mukamin sabon shugaban kasa, biyo bayan rashin amincewa da sahihancin zaben shugabancin kasar na watan Mayun bara da ya baiwa shugaba Maduro damar zarcewa bisa mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.