An fara tattaunawar neman zaman lafiyar Chadi a Qatar
Gwamnatin mulkin sojan kasar Chadi da kungiyoyin 'yan adawa da dama sun fara tattaunawar zaman lafiya a Qatar domin kawo karshen matsalar tawaye a kasar da kuma gudanar da zabe.
Wallafawa ranar:
Firaministan kasar Chadi Albert Pahimi Padacke da shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat sun shaidawa mahalarta taron cewa a ranar Lahadi cewa, dole ne bangarorin biyu su hakura da wasu daga cikin kudurorinsu domin cimma kyakkyawar matsaya.
Kungiyoyin ‘yan tawaye da na 'yan adawa 44 ne aka gayyata zuwa taron tattaunawar sulhun na Chadi da ke gudana a birnin Doha na kasar Qatar, wanda ya kamata a ce a fara gudanar da shi, daga ranar 27 ga watan Fabrairu.
Chadi ta fada cikin rudani a watannin baya bayan nan, biyo bayan kashe tsohon shugaban kasar Idriss Deby Itno yayin fafatawa da 'yan tawaye a arewacin kasar cikin watan Afrilun da ya gabata, abinda ya sanya dansa Mahamat Idriss Deby Itno, ya karbi ragamar mulkin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu