Najeriya: Ina aka kwana kan 'fyaden' da manya suka yi wa yaro a makaranta?

Akwai Ibom
  • Marubuci, Ishaq Khalid
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

A cikin 'yan kwanakin nan daya daga cikin lamuran fyade da suka dauki hankalin 'yan Najeriya shi ne wanda ake zargin an yi wa wani yaro dan shekara 11 a wata makarantar sakandare da ake kira Deeper Life High School mallakin wata majami'a. Ana zargin lamarin ya jefa yaron cikin rashin lafiya.

Shi dai dalibin karamar sakandare ne a makarantar. Ana zargin manyan dalibai ne suka yi ta lalata da yaron, a makarantar dake Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

Da farko gwamnatin jihar dake kudancin Najeriya ta bayyana cewa ta kaddamar da bincike kan zargin lalata da kankanen yaron.

To amma daga bisani gwamnatin ta ce ta fasa binciken. Ta kara da cewa tana goyon bayan tabbatar da adalci amma yanzu zata bar hukumomi na gwamnatin tarayya su yi binciken.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan dalilin hukumomin jihar na janyewa daga binciken. Sai dai an ruwaito kwamishinan watsa labarai na jihar,

Ini Ememobong, na cewa sun dauki matakin ne bisa shawarar babban lauyan gwamnati wato Atone-Janar na jihar inda za su bar ragamar binciken a hannun hukumomi na gwamnatin tarayya.

Tuni dai rundunar 'yansanda a jihar ta Akwa Ibom ta tabbatar wa BBC cewa ta fara bincike a nata bangaren.

Kakakin rundunar a jihar, Macdon Adiko ya ce ''ba zamu gajiya ba, sai an tabbatar da adalci. Duk wanda aka gano yana da hannu a lamarin, zai fuskanci shari'a.''

Ita ma makarantar ta Deeper Life ta ce ba zata yi rufa-rufa ba kan lamari, kuma zata bayar da hadin kai a duk wani bincike.

Yadda maganar boye ta fito bainar jama'a

Rahotanni dai na cewa ana yi wa yaron mai shekara 11 jinya a wani asibiti sakamakon matsalar da ya fada ciki.

Ana dai zargin cewa wasu manyan daliban makarantar sun yi ta lalata da shi ne bayan da aka sauya masa dakin kwana zuwa inda su ke.

Mahaifiyar yaron ce ta fara fito da maganar a bainar jama'a, tana mai cewa ta ga alamomin raunuka a duburan yaron sakamakon fyaden da ake zargin manyan dalibai sun yi masa.

Cikin wani sako a kafofin intanit, mahaifyar ta kuma koka kan yadda ta ce dan nata ya lalace saboda rashin samun abinci yadda yakamata..

Bayan bayanin nata ne, sai jama'a da kuma kungiyoyi suka fara bin diddigin lamarin tare da sharhi a kai. Haka kuma hukumomi suka shiga cikin lamarin tare da kaddamar da bincike.

Tun farko dai hukumomin makarantar sun dakatar da shugabar makarantar ta birnin Uyo bayan bullar rahotannin fyaden. Haka kuma makaranar ta ce ta kaddamar da bincike.

A wani bayani ta bidiyo a shafin Twitter sakatariyyar ilmi ta makarantar Mrs Thelma Malaka, ta ce su a makarantar ba su lamuntar cin zarafi, kuma suna goyon bayan bincken da hukumomi ke yi tare da fatan za a yi adalci.

Ita dai makarantar ta Deeper Life High School wadda ta wata majami'ar pentecostal ce, hedikwatarta na birnin Legas. Amma tana da rassa a sassa daban-daban na Najeriya.

Fyaden da aka yi wa dan-makarantar ya fusata 'yan Najeriya.

Fyaden da ake zargin an yi wa yaron a makarantar sanadaren ta Deeper Life High School a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom dai ya fusata jama'a da dama a Najeriya inda batun ya karade kafofin sadarwa na intanit a cikin 'yan kwanakin nan.

Mutane na ta nuna kaduwa tare da kiran a dauki kwakkwaran mataki. Rahotanni dai na cewa yanzu haka ana yi wa yaron jinya a asibiti.

Wata mai fafutikar kare hakkin bil-Adama, Mrs Precious Nwajiro, ta bayyana mamaki kan yadda lamarin ya faru a makaranta da kungiyar addini ke tafiyar da ita. Mrs Precious ta ce dole a yi bincike na gaskiya kan zargin lalatar.

Ko da yake rundunar 'yan sanda a jihar ta Akwa Ibom, ta sha alwashin cewa duk wanda aka ga yana da hannu a lamarin, za a gurfanar da shi a gaban shari'a, ta ce kawo yanzu ba a kai ga kama wani da ake zargi ba.

Wakilin BBC a Legas Umar Sheu Elleman ya ce batun yi wa dalibin fyade ya dauki hankalin mutane a ciki da wajen Najeriya, ciki har da jami'ar kare hakkin bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya.

Wakilin namu ya kara da cewa a halin da ake ciki daidaikun mutane da kungiyoyi na ta kiraye-kirayen a dauki mataki a kan batun wannan dalibi da ma matsalar fyaden baki dayanta.

Yaya girman matsalar fyade ya ke a Najeriya?

Fyaden da ake zargin an yi wa dalibin na makarantar Deeper Life, ya sake janyo muhawwara kan matsalar fyade a fadin Najeriya.

Matsalar fyade ta zama tamkar ruwan dare a kasar kuma wasu lokutan takan rutsawa ne da kananan yara - maza da mata. A wasu lokutan har kashe wadanda aka yi wa fyaden ake yi.

Ko da yake matsalar kan rutsa da maza kamar yadda ake zargin ta faru da wannan yaro dan-makaranta, to amma baki daya ta fi rutsawa da mata da kuma 'ya'ya mata.

Haka kuma lamarin kan jefa wadanda aka rutsa da su cikin yanayin tsananin tunani da damuwa na tsawon lokaci.

Samun cikakkun alkaluma na fyade a sassa daban-daban na Najeriya abu ne mai wahala,

To amma a baya Sufeto-Janar na 'yansandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya ce daga watan Janairu zuwa watan Mayun 2020, 'yan sanda sun samu rahotannin fyade 717 a fadin kasar.

Wannan na nufin akan aikata fyade akalla sau daya cikin kowace awa biyar a Najeriya. Ya kuma ce an kama mutane 799 da ake zargi.

Amma babu wani bayani dake nuna cewa cikin adadin akwai wanda kotu ta samu da laifi.

Duk da haka an yi imanin cewa adadin da ake samu a hukumance ko kadan bai kai adadin fyade da ba a bayar da rahotanninsu ba.

Masharhanta na ganin ana fuskantar matsala wajen sanin hakinannin adadin fyade da ake aikatawa ne saboda rashin kyakkyawan tsarin tattara alkaluma, da kuma rashin kai rahotannin fyade yadda yakamata a kasar.

Wata matsalar kuma ita ce ta nuna tsangwama ga wadanda aka yi wa fyade lamarin da ke sanyaya gwiwar iyaye wajen kai rahotanni idan an rutsa da 'ya'yansu.

Mene ne hukumomin Najeriya ke yi kan matsalar dungurugum?

Yayin da ake bincike kan cin zarafin yaro a makarantar kwana ta Deeper Life igh School, wani abu da ya ke tabbas shi ne cewa fyade dadaddiyar matsala ce wadda ta yi Kamari a Najeriya, wadda kuma ke bukatar tashi tsaye haikan domin dakile ta.

Hukumomi dai a kullum na cewa suna kokarin yaki da matsalar ta fyade. Misali a watan Yunin 2020 ne gwamnonin jihohin Najeriya 36 suka yanke shawarar ayyana dokar -ta-baci a kan matsalar fyade saboda muninta da kuma zanga-zanga da masu fafutika suka yi a tituna.

Jihohi da dama a kasar sun tsaurara dokokinsu na yaki da fyade da cin zarafin mata inda wasu suka tanadi hukuncin kisa.

Jihar Kaduna dake arewacin kasar ta tanadi hukuncin dandaka da kuma kisa ga duk wanda kotu ta samu da laifin yi wa yarinya ko yaro da basu wuce shekara 14 da haihuwa ba fyade.

Sai dai ana yawan samun jinkiri wajen shari'a a Najeriya kuma ba kasafai ake yanke wa masu fyade hukunci a kotuna ba, balle batun aiwatar da hukuncin.

Masharhanta da dama na ganin kokarin hukumomin bai taka kara ya karya ba wajen shawo kan matsalar fyaden musamman idan aka yi la'akari da yadda ba a cika aiwatar da dokokin da ake kafawa ba.

Hakazalika, wasu na ganin kamata ya yi a kara himma wajen wayar da kan jama'a, da ilmantar da su game da illolin fyade da hanyoyin kiyayewa.

Za a dai zuba ido domin ganin yadda lamarin dalibin na jihar Akwa Ibom da ake zargin an yi lalata da shi zai kaya, yayin da ake ci gaba da yi masa magani a asibiti, mahaifiyarsa kuma ke hankoron ganin an yi masa adalci.