Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa-Olympic

Kwallon Kafa: Ivory Coast ta rike Brazil canjaras a Olympic

Tawagar kwallon kafar Ivory Coast ta buga canjaras da mai rike da kofin wasan kwallon kafa a gasar Olympic, Brazil a ranar Lahadi, inda suka tashi wasa babu ci, a wasan kwallon kafa na maza da ke gudana a gasar wasannin motsa jiki ta Olympic a birinin Tokyo na Japan.

 Youssouf Dao au na Ivory Coast da Dani Alves na Brazil.
Youssouf Dao au na Ivory Coast da Dani Alves na Brazil. REUTERS - PHIL NOBLE
Talla

Tawagar Brazil, wadda lashe gasar kwallon kafa ta Olympic  a karon farko cikin shekaru 5 da suka wuce a gida, a lokacin da aka yi gasar a birnin Rio na daf dora kanta a turba ta zuwa matakin sili daya kwale a Yokohama, amma Ivory Coast ta hana ta.

An ma yi sa’a lamarin ya takaita a haka, saboda ta shafe tsawon sa’a guda tana wasan da mutane 10 saboda a minti na 13th aka baiwa dan wasan tsakiyar Brazil mai wasa a Aston Villa Douglas Luiz jan kati sakamakon rafke Youssouf Dao da yayi a yayin da yake daf da saka kwallo a raga.

Sai dai a kusan karshen wasan an bai wa Eboue Kouassi na Ivory Coast jan kati, lamarin da ya daidaita al’amura a tsakanin bangarorin.

Brazil ke jan ranagamar rukunin D da yawan kwallaye, gabanin wasanta da Saudiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.