Paris St-Germain 1-2 Man Utd: United ta fara Champions League da kafar dama

Marcus Rashford celebrates scoring Manchester United's late winner at Paris St-Germain

Asalin hoton, Getty Images

Marcus Rashford ya maimata cin Paris St-Germain a Gasar Champions League da Manchester United ta yi nasara da ci 2-1 ranar Talata a Faransa.

Rashford ya ci kwallon ne daf da za a tashi, kuma haka ya yi wannan bajintar wata 18 baya a filin Parc Des Princes.

Wannan nasara ta bai wa United damar fara kakar bana ta Champions League da kafar dama.

United ta fara wasan da kwarin gwiwa da ya kai ta samu fenariti, inda Bruno Fernandes ya buga aka tare, alkalin wasa ya ce golan PSG baya kan layi, Bruno ya sake a karo na biyu ya zura a raga.

Bayan da aka koma zagaye na biyu ne PSG ta kara sa kwazo har sai da ta zare kwallon, bayan da dan wasan United, Anthony Martial ya ci gida..

Mai tsaron ragar United, David de Gea ya yi kokari a karawar, inda ya hana kwallon da PSG ta yi kokarin ci ta hannun Kylian Mbappe da kuma Neymar.

Kungiyoyin na shirin tashi 1-1 ne sai Rashford ya samu kwallo daga wajen Pogba, sai ya kara ja zuwa gidan PSG daga nan ya takarkare ya buga daga yadi na 20 ta tafi a kasa ta fada raga.

A kakar 2018/19 da suka hadu a Champions League karawar kungiyoyi 16 da suka rage a wasan, PSG ta yi nasara da ci 2-1 a Old Traford, a Faransa kuwa United ta ci 3-1.

Manchester United za ta yi wasa uku a gida a jere nan gaba, da ya hada da karbar bakuncin Chelsea a gasar Premier ranar Asabar 24 ga watan Oktoba.

Ranar Laraba kuwa 28 ga watan RB Leipzig za ta ziyarci Old Traford a wasa na biyu na cikin rukuni a Gasar Champions League.

Sai kuma ta karbi bakuncin Arsenal a gasar Premier League ranar 1 ga watan Nuwamba.